DIJAH 36~40

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Na
    Feedoh✍🏻✍🏻

3⃣6⃣~4⃣0⃣

Wata yar uwar lubabatu zatayi magana suka hanata, tace yaya lubabatu wlhi duk laifinki ne dakikayi sake suka rainaki haka, lubabatu ta girgiza kai tace kekuwa Aisha ina amfanin rigima idan na biye masu, nikaina abin zai kare dan Allah kadai yasan mizasu gayama malam, dode ba dauka yakeba amma ai fitina batada wani amfani, hakadai yankawo amarya sukadinga habaice habaice ba Wanda ya tankamasu harsuka gaji suka tafi.

Cikin bacci taji malam yana lubabatu badai kinyi bacci ba, murmushi tayi tare da cewa sannu da zuwa malam yace yawwa, natadaki ko? Tace ah ah malam ba wani Abu, yakawo Leda guda ya aje Mata, tace nagode malam Allah yakara Rufa asiri, murmushi yayi tare da cewa amin saboda yanajin dadin aduar da lubabatu take mashi, yace toh Bari nabarki saida safe tace Allah yakaimu yasakai yafita,

Tunda tayi sallar asuba bata koma ba ta gyara gida tsaf ta Dora masu kalaci kokafin gari ya waye tagama komai, wanka tafito tana shiryawa malam ya shigo taduka har kasa tagaidashi ya amsa yana murmushi yace Ashe baki koma ba, tace eh malam na tsaya na gyara gida dan kar amarya tatashi taga kazanta shidai murmushi yayi, yace lubabatu Allah yamaki albarka, yasa aljanna ce makomarki,tace amin malam nagode.

Shekaru sunja inda komai yafaru gidan malam, cikiko harda rashin haihuwar larai dan shekara ta biyar suke amma ko batan wata bata tabayiba, tun abin na damunta ita da yaya lantana harsuka hakura, shiko malam baidamuba, ga wata tsana data dorama lubabatu gani takeyi kamar ita tahanata haihuwa tunda ita batayi.

Watarana malam yatashi da asuba zaije sallah, bayan yadawo sallah haryashigo cikin gida saiyaji kamar kukan jariri, komawar da zaiyi ya haska fitila wazai gani jaririne kwance yana kuka....

www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

Written by
                 Feedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180