DIJAH 41~45

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Na
    Feedoh✍🏻✍🏻

4⃣1⃣~4⃣5⃣

Malam ya haska da kyau tabbas jaririne aka ajemai, salati yayi, ya shiga gida yatado su lubabatu yace kuzo kuga ikon Allah, suna zuwa zaure sukayi turus suna bukatar karin bayani, malam yace masu nadawo masallaci ne naji kamar kuka ina haskawa naga jariri, lubabatu tace ikon Allah, itako larai cewa tayi yanzu haka wace tayi ciki tahaifeshi shine takawo nan, malam hararanta yayi yace miyasa baku kyautata zato akan mutane, wanan enma saikin bita da halin naki, Allah ya shiryaki kedai Baki ta tabe, tace idan gari ya ida wayewa saika kaishi gidan maigari, malam yace ba inda zankaishi ina nan tare dashi, lubabatu dauki Allah yabaki kuma abinda nakeso kirike amanar da Allah yabaki tana murna ta dauka tace in shaa Allahu malam, larai ko gida ta shige saboda bakin ciki, lubabatu ta dudduba tace malam ai macece yace Alhamdulillah, Allah yatayaki riko tace amin, malam yace abinda zaifaru mushiga gida idan gari yayi haske naje asibiti sugayaman abinda yaro zai dingaci tace toh, tarungumi diyarta tana murna sukayi daki.

Gari na wayewa malam ya dauki yarinya yamata huduba kana yaba lubabatu ira yasa kai yafita yace lubabatu ni natafi tace Allah yabada sa'a, bai tsaya ko inaba sai asibitin dake kauyensu nan yamasu bayani bukatarshi sukagayamai abinda zaisiya dakuma yan magunguna amma maganin kyauta suka bashi, malam baikoma gida ba sai da yagama saima baby komai na bukata, kana yadawo gida, koda yashigo gida suna tsakar gida su duka, yayi sallama lubabatu ce kawai ta amsa mai larai ko inda yake bata kallaba lubabatu tace sannu da zuwa malam yace yawwa ya diyar taki, tace gatanan lapia lau, wanka na mata bacci takeyi yace toh Masha Allah yakawo kayanta yabata yace gasunan na amfaninta ne yamata bayani yadda zatayi amfani dasu tace toh malam sannu da kokari Allah yabiyaka da gidan aljanna yace amin..

Sati yazagayo bawani taron suna akayiba andai radama yarinya suna inda taci suna Nana khadija, malam kuma ya yankama yarinya rago yashigo gida yana murna yatara matanshi, yace abinda zangayamaku shine yau yarinya tacika sati hanuna yau namata radin suna yace kuma koda wasa bansan wani yanuna banina haifeta ba hardaike larai da bakin hali yamaki yawa, yace kuma yarinya taci sunan mahaifiyata nasamata Nana khadija amma za'a dinga kiranta da dijah, lubabatu tace yayi malam Allah yabamu ikon rike amana yace Amin..

www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

Written by
                 Feedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180