DIJAH 46~50
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Na
Feedoh✍🏻✍🏻
4⃣6⃣~5⃣0⃣
Larai dai batace komaiba tanata harare harare, ta tashi tashige daki, malam girgiza kai yayi, yace lubabatu abinda nakeso dake shine ki kara hakuri akan wanda kikeyi dan nasan kina hakuri da juriya akan halayyar abokiyar zamanki dan Allah na rikeki da ki Kara, lubabatu tace in shaa Allah malam zanzama mai juriya, yace yawwa lubabatu nagode Allah yasakamaki da aljanna Firdausi tace amin, dan gaskia tanasan aduar da malam yake Mata.
Kwanaki sunja inda babu abinda yasauya gidan malam nadangane da kiyayyar da larai ke nunama lubabatu da diyarta tun dijah na yar karama tatashi da kiyayyar kishiyar marikiyarta domin larai bata mata da wasa, saidai koda gigi batayi gaban malam saboda yasha nuna mata barazana da aurenta kan dijah, shiyasa bata tsangama Mata gaban malam, tun dijah bata ganeba harta gane, dan yanzu shekaranta takwas inda take aji biyu a primary, ga malam da lubabatu sun dauki san dunia sun daura Mata, komai yasamo burinshi yakawoma dijah, haka idan yana gida dijah na nan makale dashi, wanda haka yakara jama dijah tsana wajen larai, burinta guda dijah tasan wacece ita, kuma tayi alkawarin saita gayamata wacece ita..
Dijah nada shekara goma watarana tadawo daga makaranta tazo kofar dakinsu ta tardashi kulle, tayi shiru dan dai mamarta duk inda zata saita dawo suke tafiya tare, tana nan tsaye kofar dakinsu saiga Inna larai tafito, hararanta tayi tace zonan shegia, kin zuwa tayi saboda tasan halinta, tsawa ta dakamata saida ta kusa fitsari, tazo ta kama kunnenta tarike gam tace shegia yau zakisani ba bugu ba zagi amma yau zakisan wacece ke,
Kina takama malam da lubabatu ne suka haifeki ko toh shegia basune iyayenki ba dan ke shegiyace bakida uwa bare uba yardaki uwarki tayi zauren gidannan malam ya tsinceki amma basune iyayenki ba dan ke shegiyace bakida uba, saboda sai shaggu ake yardawa, wata kara da dijah tasaki tare da faduwa kasa, daidai lubabatu na kanta, da gudu takaraso wajen datake kwance tace larai kin kasheman diya mitamaki haka?
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
Written by
Feedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment