DIJAH 51~55
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Na
Feedoh✍🏻✍🏻
5⃣1⃣~5⃣5⃣
Kururuwa lubabatu takeyi tana salati shiyajawo hankalin makota suka shigo suna tambaya lapia, lubabatu tace zuwa nayi natarda dijah kwance kuma da alamu ta kasheta, mutane suka dauka salati, lubabatu tayo kan larai ta shaketa tace wlhi dijah ta mutu ban yarda saikin bita, mi baiwar Allah tamaki marainiya da ita, tasashe da wani irin kuka, daidai nan malam na shigowa yace lubabatu lapia? Ta gwadamai dijah kwance, yamatso da sauri yace lapia mike damunta miyafaru da ita mi akamata, atare yajero mata wanann tambayoyin, lubabatu ta ce katambayi matarka, itako larai tayi tsuru tsuru batayi tsammanin abin zaikai haka ba, tsawa malam yamata yace mikika mata? Wani yace malam aceto ran yarinyar nan kana atsaya maida bayani.
Ruwa malam ya debo yayi adua ciki kana yashafa ma dijah a fuska ahankali tafara bude idanuwa harta budesu gaba daya, daya bayan daya tabisu da kallo fuskanta tasauka kan lubabatu dake sharan hawaye, tashi tayi tarungumeta tafasa kuka, tace mama dagaske baku kuka haifeniba tsintata kukayi kumani shegiya ce, dan Allah mama karki boyeman kigayaman, kuka lubabatu tasaki yace larai burinki yacika dama abinda kikeso kenan kuma kinsamu saiki zuba ruwa kasa kisha..
Malam da idonshi sukayi jah yace larai kinci amanata kuma wanan sirrin dakika fasa bazan taba yafemaki ba,kitafi gidanku nasakeki saki guda, larai tadora hannu bisakai ta kurma uban ihu tace wlhi ba inda zani aygaskia nafada ayba ku kuka haifeta ba garatasan wacece ita, mutanen dasuka shigo suka dinga tir da halin larai haka suka fita suna Allah wadaran hali irin nata.
Lubabatu ta rungume dijah suna kuka, tace kiyi hakuri diyata kada ki dauki maganar larai da gaske tayine Santa musguna maki, dijah tace mama dan Allah karki boyeman komai kigayaman wlhi Zan dauki kaddara, kuma ko kingayaman bashine zai canjaku daga mahaifana ba, daidai nan malam yayi gyaran murya yace dijah sannu da jiki, ki kwantar da hankalinki kinji, tunda kinasan kiji komai zangayamaki yanzu kuwa amma saikinman alkawari bazaki gujemu ba tace baba nayi inma nagujeku intafi ina? Aykune mahaifana dunia da lahira, malam ya kwashe abinda yafaru tundaga farko har karshe yagaya ma dijah,kuka tasaki tare da Kara kankame lubabatu tace mama nagode kwarai dagaske tabbas kincika ajinjina maki, dan kosau daya baki taba Nuna bake kika haifeni ba, nagode da gaske Allah yasakamaki da gidan aljanna,baba kaima na gode daka ceto rayuwa dabansan inda nakeba yanzu wata kilama na mutu nagode maku sosai,lubabatu ta rungumeta tana hawaye tace bakomai dijah ke diyatace dunia da lahira.
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
Written by
Feedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment