DIJAH 6~10

🏵🏵🏵DIJAH🏵🏵🏵

Na
    Feedoh✍🏻✍🏻

0⃣6⃣~1⃣0⃣

Dijah ta ce kiyi hakuri Inna wlhi bada san raina nakai marece ba, bansan da goron baneba, inna larai tace dan uwarki kina aikinmi da baki saida goro ba? Karya kike ba talla kikaje ba, kina dai dakin samarin ki gantalalla, kizo nan wlhi kokuma idan na sameki nan saina karyaki, dijah ta matsa gaban Inna larai, wani mari data mata nikaina saida na kusa kifawa, bugunta ta cigaba da yi, tun dijah na kuka tana ba Inna hakuri hartakai bata magana,

Saida Inna larai tagaji dan kanta kana ta kyale dijah, tace tashi shegiya kije ga wanke wanke can kiman, kuma kigama kije ki debo ruwa, kuma yau bazan iya baki abinci na ba, haka dijah taja jikinta tatafi tafara wanke wanke ga wata uwar yunwa tanaji, dan yau KO Karin kummalo batayiba, haka tagama aikinta tsaf kana tadauka bokoti ta nufa rafi, tana fita sukayi kicibis da hanne, itama zataje diban ruwa, da gudu hanne takaraso wajen dijah tana tambayarta lapia?, nan dijah tagaya mata yanda Inna larai ta mata, dijah tace hanne wai dagaske ni shegia ce? Kamar yadda Inna larai ke fada, hanne ta dafa dijah tace keba shegia baceba da ubanki kamar kowa, kuma in shaa Allah sai Inna taga ishara, dijah ta girgiza kai, tace wlhi hanne yau KO karyawa banyiba, hanne taja hannun dijah suka shiga gidansu, ta zubo mata abinci, nan naga dijah na hannu baka hannu kwarya,

Suna gama cin abinci suka tafi rafi diban ruwa, suna isa  rafi suka iske habu, nan yataso yana washe ma dijah baki, itako ko ajikinta hanne ce ta gaidashi ya amsa yana kallon dijah, yace ranki ya dade ba magana dijah tace hmmm, hanne ta dauka bokitin dijah ta diba ruwan, zasu taho habu ya biyosu yanama dijah magana, dijah ta juyo ba yabo ba fallasa tace habu dan Allah kayi hakuri, wlhi duk randa Inna tagane kana sona saita kusa kasheni, dan Allah karufaman asiri kayi hakuri, idanuwanta suka ciko da kwalla, taja hannun hanne suka wuce, sukabar habu nan tsaye yana tausayama dijah, saboda kaf kauyen kowa yasan halin datake ciki duk wanda yayi niyar taimaka sai Inna tarabasu, hanne ce kawai bata rabasu ba, saboda maman hanne itama batada wasa dole yasa Inna larai takyale dijah da hanne, saidai hanne ko zauren gidansu dijah bata shiga saboda gudun rigima, akwai inda suke haduwa idan sun fito..

Haka suka taho hanne na kara kwantarma da dijah da hankali, harsuka iso gida, kowace tayi hanyar gidansu, dijah ta shiga gida da sallama, goggo na nan inda tabarta wata harara ta aikamata tare da jan tsaki, tace shegia maikama da diyar mayu, nidai da in haifi irinki gara da ban haihuba dan haihuwar irinku masifane, kina wucewa daga gabana dan ubanki kinzo kin man tsaye da bokiti Kai....

Written by

               Feedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180