DIJAH 61~65

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Na
    Feedoh✍🏻✍🏻

6⃣1⃣~6⃣5⃣

Tsaye tayi zaure tabi gawan da Ido,da alamu k'arin bayani take nema, takasa d'aga kafanta, ita bata shiga gidaba itakuma batayi wajeba,"tana nan tsaye zaure aminiyar lubabatu ta fito ganin dijah tayi tsaye, "hanunta takama tayi cikin gida da ita, binta dijah tayi kamar rak'umi da akala, har suka isa d'akin lubabatu,"mutane naganin dijah sukafara kuka, " itadai takasa fassara kukan da sukeyi, bin d'akin tayi da kallo,"amma bataga mamantaba," I don't a tasauke kan kawar mamanta, "dijah tace mama Aisha ina mamana take? ,"kuka Aysha tasaki mai k'arfi, tajawo dijah jikinta," tace khadija kiyi hakuri ki d'auki dangana kinsan Allah baya barin wani dan wani yaji dad'di, wannan lokacin ne zakima marainiya, kirik'e maraicinki kiyi hakuri da k'addararki,kodingama mahaifiyarki adua, "mahaifiyarki sunanki ne bakinta har ta daina numfashi," wani razana da dijah tayi tafara salati, "rik'ota Aysha tayi tazaunar da ita,"dijah tace haba mama yazakiman haka, yaxakibarni cikin wannan duniyar maicike da k'alubale, kinsan banda wani gata saike, kece jigon rayuwata kece gatana, kece bangon dana dafa yau gashi ya rushe, yau gashi kintafi kinbarni taya zan k'arasa rayuwa ahaka, duk wanda ke d'akinan ba wanda baima dijah kuka ba, tashi tayi tsaye, tana mikewa ta sulale tafad'i k'asa

********************
Rud'ewa sukayi wata aminiyar marigayiya ce ta d'auko ruwa ta watsamata amma ina dijah tayi nisa ko motsi batayi, "babu wata dubara da basuyiba amma shiru, "ayshace taje ta Kira malam tagayamai abinda ke faruwa, "dasauri malam ya shigo d'akin ganin dijah kwance kamar gawa yasashi rud'ewa dama ga wadda yake ciki narashin matar kwarai, "kinkimarta yayi yafita waje da ita Aysha na biye, mota akasa dijah sai asibiti.

Likitoci ukku kan dijah amma ina ko numfashi batayi, sukansu likitocin sunfara fidda rai, "malam kuwa inbanda adua ba abinda keyi, Aysha kuwa inbanda kuka ba abinda takeyi,"dakyar numfashin dijah yafara dawowa, ahankali tafara kad'a hanunta murna likitoci sukafarayi, ahankali hartafara bud'e Idonta, "da mama ta farka a bakinta tana mama kidawo karkiman man haka kitaimaki rayuwana," allura likita yamata ta bacci, kana suka fita, "likita yacema malam yasameshi office...

www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

Written by
           Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180